Home Labaru Kawo Cigaba: Najeriya Da Amurka Za Su Kulla Wata Dangantaka

Kawo Cigaba: Najeriya Da Amurka Za Su Kulla Wata Dangantaka

198
0

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ya ce hadin gwiwar Najeriya da kasar Amurka zai taimakawa wajen ciyar da kasashen biyu gaba a bangarori da dama.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin mai taimakawa Osinbajo kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Laola Akande.

Laola Akande

Osinbajo ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban hukumar kula da ci gaban kasashe na kasar Amurka Mark Green a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Osinbajo ya ce kasar Amurka na daya daga cikin kasashe da Najeriya ke hulda ta kud da kud da ita akan abubuwan da suka shafi ci gaba.

Ya ce gwamnatin tarayya na matukar godiya da irin gudunmawar da kasar Amurka ta ba da a bangaren kula da lafiya, agajin gaggawa da kuma bangaren ilimi.

Sannan ya jaddada kudurin gwamnatin shugaban shugaba Buhari na kara inganta bangaren ilimi ta hanyar samar da ilimin kyauta a matakin farko da kuma maida sanya yara a makarantu wajibi.

A nasa jawabin jagoran tawagar ‘ya ce Najeriya da kasarsa ta Amurka, za su ci gaba da aiki tare da kuma musayar ra’ayoyi domin samun ci gaba.