Home Labaru Tsaro: Rundunar Yan Sanda Ta Ceto Mutane 22 Da Aka Yi Garkuwa...

Tsaro: Rundunar Yan Sanda Ta Ceto Mutane 22 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Imo

217
0

Rundunar yan sandan Operation Puff Adder a jihar Imo ta gurfanar da mutane 72 da ke da hannu a laifuka daban-daban da aka aikata kwanan nan a jihar.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Rabiu Ladodo

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Rabiu Ladodo ya bayyana cewa an kama masu laifin ne a yankuna daban-daban a jihar cikin makonni shida da suka gabata.

Har ila yau an kama wani mamban na kungiyar miyagu masu yiwa mata fyade, Stanley Ebere wanda ya kasance da hannu cikin fyade da aka yi ma wata yarinya yar shekara 11 a gaban sauran mambobin kungiyar.

A cewar shi, farautan ‘yan fashi a jihar ya kasance manufar “Operation Puff Adder” wanda Sufeto Janar na ‘yan sanda ya kaddamar, wanda ya ce har ila yau tana nan daram. Ya kara da cewa an ceto wasu mutane 22 da aka yi garkuwa da su, yayin da aka kwato motoci 11.

Ladodo, ya bayyana cewa daga cikin wadanda aka gurfanar akwai mambobin kungiyar gawurtaccen mai garkuwa da mutanen nan da ya shahara a harkar sace kananan yara daga gidajen su.

A cewar kwamishinan ‘yan sanda, rundunar na nan tana bin duddugen mambobin kungiyar da suka tsere, yayin da ake kokarin ganin an kubutar da yaran da aka sace.