Home Labaru Labarun Ketare Zaben Tunisia: Masu Yakin Neman Zabe Su Rufe Zagayen Sun A Neman...

Zaben Tunisia: Masu Yakin Neman Zabe Su Rufe Zagayen Sun A Neman Kuri’u

216
0
Zaben Tunisia: Masu Yakin Neman Zabe Su Rufe Zagayen Sun A Neman Kuri’u
Zaben Tunisia: Masu Yakin Neman Zabe Su Rufe Zagayen Sun A Neman Kuri’u

‘Yan takarar shugaban kasa a Tunisia suka rufe yakin neman zaben da suke gudanar kafin zaben kasar na ranar lahadi wanda ke cike da rashin tabbas.

A ranar juma’ar da ta gabata ne aka rufe yakin neman zaben, wanda ake sa ran kotun daukaka kara ta zartar da hukunci a kan karar da aka shigar kan Nabil Karoui, daya daga cikin ‘yan takarar, wanda tun ranar 23 ga watan Agusta ya ke rufe a kurkuku sakamakon zargin sa da halatta kudaden haram.

Nabil Karoui,  dan kasuwa ne da ke yawan sukar gwamnati, inda ya ke zargin ta da yin amfani da kotu domin hana shi tsayawa takara.

Magoya bayan Nabil Karoui,  sun yi alkawarin gudanar da zanga-zanga a gaban harabar gidan kurkukun da ke Monarguiba, kilomita kadan da Tunis babban birnin kasar ta Tunisiya.