Home Labaru Batun Makamai: Amnesty Ta Roki MDD Kada Ta Cire Takunkumin Da Ta...

Batun Makamai: Amnesty Ta Roki MDD Kada Ta Cire Takunkumin Da Ta Sawa Sudan Ta Kudu

150
0

Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International, ta buƙaci Majalisar Ɗinkin Duniya da kada ta cire takunkumin da ta sa wa Sudan Ta Kudu kan makamai, a daidai lokacin da dakarun gwamnati ke ƙara kai hare-hare da ci gaba da far wa farar hula da kuma aikata laifukan yaƙi.

Ƙungiyar ta amnesty ta ce tana da hujjar cewa dakarun gwamnati da na tsoffin yan adawa sun aiwatar da wasu kashe-kashe da aka yi ba bisa ƙa’ida ba da raba mutane da muhallansu da azabtarwa da kuma lalata gidajen fararen hula.

Ƙungiyar ta bayyana cewa rikicin da ake samu a jihohin Jonglei da Lakes da Warrap da Western Equatoria ya ninka sau huɗu tsakanin Afrilu zuwa Yunin wannan shekara, idan aka kwatanta da shekarar bara.