Home Home Takara: Kwankwaso Ya Ce Ya Fi Tinubu Da Atiku Ilimi

Takara: Kwankwaso Ya Ce Ya Fi Tinubu Da Atiku Ilimi

160
0
Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa ƴan takarar shugaban kasa na APC wato Bola Tinubu da na PDP Atiku Abubakar duk ruɓaɓɓun ƴan siyasa ne sun riga sun gaji.

A hira da ɗan takarar yayi da radiyon Alfijir, ya yi kakkausar suka ga takarar Atiku Abubakar na PDP da Bola Tinubu na APC.

Kwankwaso ya ce Mutanen biyu sun gaji ba za su iya ba, ya ci gaba da yi wa ƴan Arewa gargaɗin kada su yi kuskuren sake zaɓen wanda zai gasa musu wuta a hannu.

Kwankwaso ya ja hankali da kira ga ƴan Najeriya su tabbata sun zaɓi nagari wanda ,ai ji tausayin su ya kuma samar musu da ababen more rayuwa sannan kum mai kishin su.

Leave a Reply