Home Home Rikicin APC A Kano: Tinubu Da Shekarau Sun Tattauna

Rikicin APC A Kano: Tinubu Da Shekarau Sun Tattauna

62
0

Jiga-jigan jam’iyyar APC, tsohon gwamnan jihar Lagos, Bola Ahmed Tinubu da tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau sun gana a karon farko tun bayan rikicin da ya barke a jam’iyyar reshen jihar Kano.

Rikicin , wanda ya sa Shekarau da wasu ‘yan majalisar dokokin tarayya na jihar ta Kano ballewa daga bangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje suka kira kansu G-7, ya kuma sa bangarorin biyu kowanne ya gudanar da zabukan shugabannin jam’iyyar na jiha.

A bangaren Gwamna Ganduje, an zabi Abdullahi Abbas a matsayin shugaban APC na Kano, yayin da a bangaren Sanata Shekarau aka zabi Ahmadu Haruna Zago a matsayin shugaban jam’iyyar.

Wadannan zabuka sun raba kan ‘yan jam’iyyar ta APC a jihar Kano, wadda ta fi yawan al’umma a arewacin Najeriya.

 Hasalima rikicin ya kai ga Ganduje da Shekarau suna yi wa juna shagube.