Home Labaru Bukukuwan Sallah: An Bukaci Iyaye Su Kula Da Motsin ‘Ya’yan Su

Bukukuwan Sallah: An Bukaci Iyaye Su Kula Da Motsin ‘Ya’yan Su

654
0

A daidai lokacin da za a fara gudanar da bukukuwan babbar Sallah,  an ja hankalin iyaye su, sa Ido  akan ‘ya’yan su, domin a wannan lokacin ne miyagu ke amfani da shi wajen cutar da Yara.

Alhaji Ali Sokoto

Kwamandan kungiyar ‘yan sintiri ta Nigeriya Alhaji Ali Sokoto ya bayyana haka a cikin sakon sa na barka da  Sallah.

Ya ce akwai bukatar iyaye su san wuraren da ‘yaran su ke zuwa domin guje wa yadda miyagu ke amfani da lokacin Sallah sun a satar yara ko aikata ta’addanci da su.

Ali Sokoto ya kara da cewa,  a wannan lokacin ne ake bukatar matakan tsaro a kowane bangare domin kare rayuka da dukiyoyin Al’umma, don haka ya umurci kwamandojin su na Jihohi 36 na Nijeriya  su kara azama wajen  daukar matakan tsaro  a fadin Nijeriya.