Home Labaru Sauyin Sheka: Sama Da Mutane 6000 Sun Bar Jam’iyyar APC Zuwa PDP...

Sauyin Sheka: Sama Da Mutane 6000 Sun Bar Jam’iyyar APC Zuwa PDP A Jihar Zamfara

568
0

Shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaba Buhari na shekara ta 2019 a jihar Zamfara Alhaji Bature Sambo da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC sun sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.

Da ya ke jawabi yayin da su ke sauya shekar a gidan gwamnatin jihar Zamfara, Sambo ya ce yanayin aikin gwamnan jihar Bello Matawalle ne ya sa ya yi sha’awar barin jam’iyyar APC.

Bature Sambo ya kara da cewa, tsohon gwamnan jihar Abdul’aziz Yari ya kasa yin abin da gwamna Matawalle ya yi a yanzu.

Sambo dai ya sauya shekar ne tare da shugaban gudanarwa na asibitin tarayya da ke Port Harcourt Alhaji Muktari Anka, da Alhaji Abdullahi Mohammed, da Alhaji Ibrahim Ajala da kuma sama da mutane dubu shida ‘yan jam’iyyar APC.

Da ya ke karbar masu sauya shekar, Gwamna Matawalle ya ce ba za su nuna bambanci tsakanin su da tsofaffin jam’iyyar PDP ba.