Home Labaru ‘Yan Sandan Sun Ce Mota Ce Ta Buge Dan Jaridar Na Vanguard

‘Yan Sandan Sun Ce Mota Ce Ta Buge Dan Jaridar Na Vanguard

114
0

‘Yan sandan Najeriya sun tabbatar da mutuwar ɗan jaridar nan Tordue Henry Salem bayan ya ɓata tun ranar 13 ga watan Oktoba.

Kafin mutuwar sa, Tordue Henry Salem wakilin jaridar Vanguard ne a Majalisar Wakilai.

Yayin wani taron manema labarai a nan Abuja a ranar Juma’ar nan, ‘yan sanda sun ce mota ce ta bige shi, kazalika, sun gabatar da wani mutum da ake zargin shi ne direban motar.

An ga gawar Tordue Henry  ne kwana biyu bayan Majalisar Wakilai ta bayar da umarnin gudanar da bincike kan ɓatar sa.

Yanzu haka gawar sa tana dakin ajiye gawa na Babban Asibitin Wuse da ke nan Abuja.

Leave a Reply