Home Labaru Na Daina Zuwa Jaje A Zamfara – Yariman Bakura

Na Daina Zuwa Jaje A Zamfara – Yariman Bakura

1252
0
Ahmed Yariman Bakura, Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara

Tsohon gwamnan jihar Zamfara Sanata Ahmed Yariman Bakura, ya yi Karin haske a kan dalilin da ya sa bai damu da zuwa jajenta wa mutanen da kashe-kashen da ake yi a jihar ya shafa ba.

Yariman Bakura ya shaida wa manema labarai cewa, akwai abubuwan da su ka fi zuwa jaje muhimmanci da ya kamata shugabanni su maida hankali a kai.

Ya ce a baya ya fara zuwa jaje, amma bayan ya lura da cewa abu ne da ake yi kullum, sai ya koma bada shawara game da matakan da ya kamata a dauka, amma ya ce zuwan sa jaje ba zai kawo karshen matsalar tsaro a jihar ba.

Karanta Labaru Masu Alaka: Yariman Bakura Ya Sha Alwashin Ba Matawalle Goyon Baya

Jihar Zamfara dai ta na daga cikin jihohin arewa maso yamma da ake yawan samun kashe-kashe da sace-sacen mutane, lamarin da ke jefa mazauna yankin cikin fargaba da raba wasu da muhallan su.

‘Yan Nijeriya da dama dai sun dade su na alakanta matsalolin tsaro da rashin samun shugabanci nagari tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya, sai dai Yariman Bakura ya ce ce talauci ne ya jefa jihar cikin halin da ta ke ciki a yau.