Tsohon ministan Sufuri kuma jigo a jam’iyyar PDP a da, Femi Fani-Kayode, ya bayyana komawar sa jam’iyyar APC da cewa ita kadai ce hanyar da iya saka wa irin Nasarorin da gwamnatin shugaba Buhari ta samu.
A jawabin da ya yi wa manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja, Kayode ya ce ya koma jam’iyyar APC ne don ya hada hannu da gwamnatin shugaba Buhari a ciyar da Nijeriya gaba.
Ya ce shugaba Buhari ya taka rawar gani a Nijeriya, musamman a fannin harkar samar da tsaro.
Fani-Kayode, ya ce ita siyasa da ma haka ta gada, duk inda mutum ya ga nan ne ci-gaba ya karkata zuwa can idan har dan kishin kasa ne na gaske.
Gwamnan jihar Yobe Mala Buni, ya ce shugaba Buhari ya yi matukar Farin ciki a kan wannan gagagumin kamu da jam’iyyar APC ta yi.

