Home Labarai Majalisar Wakilai Ta Roki China Ta Taimaka A Kubutar Da Fasinjoji Da...

Majalisar Wakilai Ta Roki China Ta Taimaka A Kubutar Da Fasinjoji Da Aka Sace

84
0

Kwamitin kula da harkokin sufuri na majalisar wakilai, ya roki gwamnatin kasar China ta taimaka wajen ganin an kubutar da fasinjojin jirgin kasa da aka sace a kan hanyar su ta zuwa Kaduna daga Abuja.

Shugaban kwamitin Sanata Abdul-Fatai Buhari ya bayyana haka, yayin wata ziyarar gani da ido da kwamitin ya kai tashar jirgin kasa ta Obafemi Awolowo da ke Ibadan, inda ya bayyana rashin jin dakin sa a kan rashin kubutar da mutanen har zuwa yanzu.

Sanatan, ya ce harin da aka kai a kan jirgin kasan ya sanya fargaba a zukatan ‘yan Nijeriya, wadanda su ka koma tafiye-tafiye ta hanyar shiga jirgin.

Ya ce ba laifi ba ne idan gwamnatin kasar China ta zo ta taimaka wa Nijeriya wajen ceto fasinjojin da aka sace.