
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sa hannu a kan kudurin lafiyar kwakwalwa da aka gabatar tun cikin shekara ta 2021 bayan ya kasa tsallake muhawara tun a shekara ta 2003 zuwa 2013.
Majalisun dokoki na tarayyar Nijeirya dai sun yi muhawara a a kan kudurin a shekara ta 2021.
Shugaban kwamitin harkokin lafiya na majalisar dattawa Sanata Ibrahim Oloriegbe ne ya tabbatar da amincewa da kudurin da shugaba Buhari ya yi a shafin sa na twita.
Kudurin dai, zai tabbatar da ganin cewa masu lalurar kwakwalwa su na da damar irin jinyar da za a yi masu kuma babu tirsasawa.
Wasu abubuwa da ke kunshea cikin dokar, sun haɗa da samar da asusun lafiya na masu lalurar kwakwalwa, da kirkiro da sashen lafiya a ma’aikatar lafiya ta ƙasa da kuma kirkiro kwamitin sa ido a kan masu lalurar da sauran su.
You must log in to post a comment.