Home Home An Sako Mamallakin Tashar Ait, Dokpesi

An Sako Mamallakin Tashar Ait, Dokpesi

26
0
Hukumomi a ƙasar Birtaniya sun sako shugaban kamfanin sadarwar na DAAR, kuma mamallakin gidan talabijin na AIT Raymond Dokpesi, bayan an tsare shi a filin jirgin sama na ƙasar a ranar Lahadin da ta gabata.

Da ta ke tabbatar da sakin sa a cikin wata sanarwar da ta fitar, hukumar kamfanin DAAR ta ce an tsare Raymond Dokpesi ne saboda wani al’amari da ya taso.

Ta ce an riƙe shi na wasu sa’o’i kafin daga bisani jami’an hukumar shige da fice na Birtaniya su buga wa fasfo sa kan-sarki na shiga ƙasar.

A karshe ta ce Raymond Dokpesi ya na godiya, dangane da ƙauna da addu’o’in da aka yi ma shi bayan samun labarin abin da ya faru shi.