Home Home Sauya Fasalin Kuɗi: Jihohin Kaduna Da Kogi Da Zamfara Sun Kai Gwamnatin...

Sauya Fasalin Kuɗi: Jihohin Kaduna Da Kogi Da Zamfara Sun Kai Gwamnatin Tarayya Ƙara

98
0
Gwamnatocin jihohin Kaduna da Kogi da Zamfara, sun maka gwamnatin tarayya Kotun Ƙoli, su na neman ta dakatar da gwamnatin tarayya aiwatar da tsarin wa'adin amfani da tsofaffin takardun kuɗi da Babban Bankin Nijeriya ya ɓullo da shi.

Gwamnatocin jihohin Kaduna da Kogi da Zamfara, sun maka gwamnatin tarayya Kotun Ƙoli, su na neman ta dakatar da gwamnatin tarayya aiwatar da tsarin wa’adin amfani da tsofaffin takardun kuɗi da Babban Bankin Nijeriya ya ɓullo da shi.

Buƙatar da lauyan jihohin uku AbdulHakeem Uthman Mustapha ya gabatar wa kotun, ta nuna cewa jihohin su na buƙatar Kotun ta hana gwamnatin tarayya da bankin CBN aiwatar da tsarin daina amfani da tsofaffin takardun kuɗin.

Masu shigar da ƙarar, sun haɗa da kwamishinonin shari’a na jihohin uku, yayin da ministan shari’a Abubakar Malami ke wakiltar gwamnatin tarayya a shari’ar.

Sun ce tun bayan bayyana fara amfani da sabbin takardun kuɗin ake samun matsalar ƙarancin sabbin kuɗi a jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara.

A karshe sun ce wa’adin kwanaki 10 da gwamnatin tarayya ta ƙara ba zai isa wajen warware matsalar da ake fuskanta ta ƙarancin takardun kuɗin ba.

Leave a Reply