Home Labaru Ilimi Buhari Ya Gaza Cika Alkawarin Da Ya Dauka A Ɓangaren Ilimi A...

Buhari Ya Gaza Cika Alkawarin Da Ya Dauka A Ɓangaren Ilimi A Kasafin 2022

13
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gaza cika alkawarin da ya dauka na kara yawan kudaden da zai kashe a fanin ilimi da kashi 50 cikin 100 nan da shekaru biyu masu zuwa, kamar yadda bayanan kasafin kudi na shekara ta 2022 da ya gabatar wa majalisa ke tabbatarwa.

Idan dai ba a manta ba, shugaba Buhari daiya alkawarta hakan ne yayin taron ilimi na duniya da ya gudana a London, inda ya bi sahun sauran kasashen duniya wajen sanar da alkawurran inganta fannin ilimi da karin kudaden da ake warewa.

Masu sharhi a kan kasafin shekara ta 2022 dai su na cewa, shugaba Buhari ya ware wa fanin ilimi Naira Biliyan 875 da Miliyan 925 da dubu 404da 37, ciki har da kudaden da aka ware wa tsarin ilimin bai-daya na UBEC Naira Biliyan 139 da Miliyan 236 da dubu 349 da 701 a cikin kasafin Naira Tiriliyan 16 da Biliyan 900 da ya gabatar wa majalisa.

Wannan dai na nufin, ɓangaren ilimi an ware ma shi kashi 5.3 cikin 100, wanda ke nuna an sake samun koma-baya idan aka kwatanta da kashi 5.6 cikin 100 na kasafin shekara ta 2021.