Home Labaru El-Rufa’I Ya Yi Wa Kwamishinoni Da Manyan Jami’An Gwamnati Garambawul

El-Rufa’I Ya Yi Wa Kwamishinoni Da Manyan Jami’An Gwamnati Garambawul

14
0

Gamnatin jihar Kaduna, ta yi ma wasu kwamishinoni da manyan jami’an ta sauye-sauyen wuraren aiki.

Gwamna Nasir El-Rufa’i, ya ce an yi sauye-sauyen ne domin kara wa bangaren gwamnati azama, tare da ba kwamishinonin damar samun fahimtar dukkkan bangarorin aikin gwamnati.

Wata sanarwa da aka fitar daga Gidan gwamnati na Sir Kashim Ibrahim, ta ce 8 daga cikin kwamishinoni 14 ne kawai sauye-sauyen su ka shafa, amma bai shafi ma’aikatun kudi da lafiya da shari’a da ma’aikatar gidaje da raya birane da ta tsaro da harkokin cikin gida da ta walwala da jin dadin al’umma ba.

Shugaban ma’aikata Muhammad Sani Abdullahi ya koma ma’aikatar kasafi da tsare-tsare, mukamin da ya taba rikewa a lokacin mulkin El-Rufa’i na wa’adin farko.

Wannan dai shi ne karo na biyu da ake sauya wa shugaban ma’aikata matsayi zuwa mukamin kwamishina, inda ko a shekara ta 2019 an sauya wa shugaban ma’aikata na wancan lokacin Muhammad Bashir Sa’idu matsayi zuwa kwamishinan kudi.