Home Labaru An Kashe ‘Yan Bindiga 32 Da Ke Tserewa Daga Zamfara A Jihar...

An Kashe ‘Yan Bindiga 32 Da Ke Tserewa Daga Zamfara A Jihar Neja

19
0

Rundunar tsaron Nijeriya, ta ce an kashe ‘yan bindiga 32 a wasu hare-haren da ta kai a kan maharan da ke tserewa daga jihar Zamfara zuwa jihar Neja.

Wata majiya ta ce, an kashe ‘yan bindigar ne bayan harin da su ka kai a shingen binciken jami’an tsaro, wanda yay i sanadin rasa rayukan ‘yan sanda biyar.

Lamarin dai ya faru ne a yankin Bangu Gari da ke karamar hukumar Rafi ta Jihar Neja.

Mijiyar tsaro ta tabbatar wa manema labarai cewa, maharan da ke tserewa daga jihar Zamfara saboda tsananin hare-hare ya na janyo tada zaune tsaye a yankunan jihar Neja.

Gungun maharan dauke da manyan makamai ciki har da roka, su na kaurace wa maboyar su da ke Danjibga da Munhaye na karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.