Home Labaru Tsokaci : Budaddiyar Wasika, Zuwa Ga Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje

Tsokaci : Budaddiyar Wasika, Zuwa Ga Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje

1017
0

Daga: Jibrin Ibrahim

Wadda Aliyu Abdullahi Gora II ya Fassara

Wasikar neman bahasin da ka aike wa mai martaba sarkin Kano ce ta janyo hankali na, inda ka bukaci ya gaggauta amsa ta a cikin sa’o’i 24, sakamakon rahoton hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano.

Duba da Kalamai, da duk abubuwan da wasikar ta kunsa, ya nuna karara cewa, akwai tunanin daukar matakin gaugawa a kan rahoton, shi ya sa na yanke shawarar rubuta maka wannan budaddiyar wasika.

Tun daga ranar 8 ga watan Mayu na shekara ta 2019, Birnin Kano ya shiga cikin halin rashin tabbas, biyo bayan matakin da gwamnatin ka ta dauka na farraka masarautar Kano.

Wannan mataki ya na da matukar hadari ga al’ummomin Kano, don haka na ke rokon ka arziki, da ka janye wannan yunkuri, saboda wadannan dalilai.

Na farko dai, Nijeriya ta na fama da barazanar tsaro a sassa daban-daban na kasar nan, kuma hankalin jami’an tsaron mu, ya karkata ne kacokam, wajen tabbatar da kawo karshen wannan barazana.

Kano, Birni ne da ya kasance mai dadadden tarihi, kuma amintacce, wanda al’ummomin cikin sa ke zaune da juna lafiya tsawon shekaru aru-aru da su ka wuce.

Ya na da matukar mahimmanci a matsayin ka na gwamna, ka kasance a sahun gaba, wajen tabbatar da zaman lafiya.

Bai dace ka dauki duk wani matakin da zai iya wargaza kyakkyawar zamantakewar al’umma ba, kuma ka na da kyakkyawar masaniyar cewa, wargaza masarautar Kano, na iya zama ummulhaba’isin tunzura al’umma, har ta kai ga lalata dadaddiyar zamantakewar da ke tsakanin su.

Ya kai mai girma gwamna, kada ka manta, wannan aniya ta farraka masarautar Kano, an sha yunkurin aiwatar da ita a lokutan baya.

A ranar 1 ga watan Afrilu na shekara ta 1981, tsohon gwamnan jihar Kano Abubakar Rimi, ya kirkiri wasu tsirarun masarautu, da ya sanya su a matsayi daya da masarautar Kano, wadanda su ka hada da Auyo, da Dutse, da Gaya, da kuma Rano.

Ya kasance Sarakunan sun yawaita a tsohuwar jihar kano, bayan an daga darajar wasu Sarakuna masu daraja ta biyu, zuwa daraja ta daya, wadanda su ka hada da Hadejiya, da Gumel, da kuma Kazaure.
A wancan lokacin, sai Abubakar Rimi ya maida sarakunan tamkar ma’aikatan gwamnati, da su ke aiki a karkashin ikon shugabannin kananan hukumomi.

A ranar 7 ga watan Afrilu na shekara ta 1981, sakataren gawamnatin jihar Kano ya aike wa sarkin Kano da wasika mai dauke da sakonni kamar haka:

“Na rubuto maka wannan wasika ne, bisa umurnin gwamnan jihar Kano Alhaji Abubakar Muhammad Rimi, domin sanar da kai, game da rashin jin dadin sa da gwamnatin jihar Kano, bisa yadda ba ka daukar umurnin gwamnati da mahimmanci.

Ya kamata a ce ka kasance mai girmama zababbiyar gwamnati, wadda ita ke da ikon tagfiyar al’amurran shugabancin al’umma, kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanada.

An kuma fahimci cewa, tun kafuwar wannan gwamnati a shekara ta 1979, akwai alamomin da su ka nuna rashin biyayyar ka ga gwamnatin jihar Kano.

Sakamakon haka, mai girma gwamnan jihar Kano ya umurce ni, in sanar da kai cewa ka kare kan ka game da wadancan zarge-zarge a cikin sa’o’i 48, ka kuma bayyana abin da zai hana a dauki matakin ladaftar da kai.

Biyo bayan wannan wasika a ranar 10 ga watan Yuli ta shekara ta 1981, ya sa ‘yan daba su ka tada kayar baya, har su ka hallaka rayukan mutane 34, su ka kuma kona wasu kamfanonin yada labarai da su ke zagin gwamnatin jihar Kano ta na amfani da su wajen yada farfaganda, ciki kuwa har da gidan rediyon Kano, da kuma ofisoshin jaridar Triumph.

‘Yan dabar, sun kuma zakulo inda Dr Bala Usman ya ke su ka kashe shi, wanda ya kasance mai ba gwamnan jihar Kano shawara a kan harkokin siyasa a wancan lokacin, kuma wanda ya rubuta wasikar da za ta iya sa a tsige sarkin daga gadon sarauta.

Sama da makonni biyu da su ka gabata, al’amurran dabanci sun yawaita a birnin Kano, kuma babu wanda ke da ra’ayin haddasa abin da zai saba wa ka’idar doka da oda.

Na biyu, masarautar Kano ta na dauke da dadadden tarihin da bai kamata a rusa shi a gaban idon ka ba. Zai zama mummunan tarihi, a ce kai ne musabbabin wargaza kyakkyawan tarihin masarautar Kano nan gaba.

Masarautar Kano ta kasance tun a shekara ta 999 bayan mutuwar Annabi Isa, kuma ta na daga cikin Daular Usmaniyya, bayan jihadi daga shekara ta 1804 zuwa shekara ta 1807.
Ta kuma kasance daya daga cikin manyan masarautun Daular Umaniyya, a karkashin ikon mai martaba Sarkin Kano, mai kula da dukkan sassan da ake kira jihar Kano a yau.

Kano, ya kasance birni ne, da ya kunshi al’ummomi masu al’adu daban-daban a Nijeriya, da ma yankin Afrika baki daya.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I, shi ne sarkin Kano na 57, ya kuma dauki dawainiyar tabbatar da tarihi, wanda ake kallo a matsayin na biyu ta fuskar al’amurran addinin musulunci a Nijeriya, baya ga mai alfarma sarkin musulmi.

Matsayi ne na addini, kuma ya na taka gagarumar rawa ta fuskar tafiyar da hukumomin siyasa, kuma ya na bada gagarumar gudunmuwa wajen tafiyar da harkokin shari’a da sauran al’amurran shugabanci.

Don Allah mai girma gwamna, kada ya kasance kai ne ummulhaba’isin rusa wannan dadadden al’amari.

Na uku, ya kamata ka janye kudirin ka, domin girmama tsarin doka. Sannan kada ka manta, a ranar 23 ga watan Mayu, Mai shari’a Badamasi, ya dakatar da gwamnatin Kano daga daukar duk wani matakin aiwatar da sabbin masarautu, da kuma matsayin dokar da majalisar dokoki ta jihar Kano ta kafa, ko kuma yin duk wani abu da zai shafi manyan masu rike da mukaman sarautun gargajiya, ko kuma sarki da kan sa, har zuwa lokacin da aka saurari karar da ta bukaci hakan a gaban kotu.

Sannan akwai shari’u biyu yanzu haka a gaban kotu, don haka bai kamata a ce gwamna ya yi fatali da umurnin Kotu ba.

Sannan kamar yadda aka tattauna a gaban kotu, akwai yiwuwar al’ummar Kano su shiga wani mawuyacin hali, matukar ba ka janye wannan kudiri na ka ba.

A bayyane ta ke, matakin da majalisar dokoki ta jiha ta dauka na ganin za ta iya kafa sabbin masarautu, akwai rashin fahimtar cewa Masarautar Kano, sarauta ce mai zaman kan ta.

Babu wata dokar da za a ce ita ta kafa masarautar Kano, wadda ta dade shekaru aru-aru, kuma jama’ar Kano su ka rungume ta a matsayin gado.

Yanayin yadda ‘yan majalisar Kano su ka yi gaugawar amincewa da waccan doka a cikin sa’o’i 48, wanda ya hana lokacin jin ra’ayoyin al’umma, da kuma yadda ka yi fatali da umurnin kotu, domin ka samar da sabbin sarakunan, duk da cewa kasan maganar ta na gaban kotu, hakan bai dace da mutum mai matsayin gwamna ba.

Kamar yadda ‘yan majalisar jiha su ka yi ja-in-ja a dokar da su ke ikirarin sabuntawa, gaba daya sun cire sashen da ke da nasaba da zaben sarki, ta hanyar musanya shi da sashe na uku a sabuwar dokar, wanda ya ke magana kawai a kan kirkirar majalisar sarakunan gargajiya, da kuma kirkirar sabbin masarautu hudu.

Babu wani bangare na sabuwar dokar, da ya ba gwamna ikon zabe, ko kuma tabbatar da nade-naden da masu nadin sarauta su ka yi.
Sannan babu wata shaidar da ta tabbatar da cewa akwai ma masu nadin sarautar a sabbin masarautun, ballantana a ce sun hadu, sun kuma yi nadi, har su ka nemi amincewar gwamnan.

A mataki na shari’a, kudirin ka ba ya da tushe balle makama, don haka ya zama wajibi ka canza ra’ayi.

A karshe, zargin almundahanar kudade da ake yi wa sarkin Kano ba ya da wani inganci, sai dai idan wani salo ne kawai neman sanadin tsige mai martaba Muhammad Sanusi daga karagar mulki.

Kamar yadda masu hikima ke cewa, mai gidan gilashi ba ya jimirin jifa. Al’ummar jihar Kano su na sane da ainihin wani zargin cin hanci da ke kunshe a faifan bidiyo.

Mai girma gwamna, ina rokon alfarmar ka duba wadancan batutuwa hudu da idon basira, tare da fatan hakan zai ba ka damar yin kyakkyawan nazari, ka janye kudirin ka na wargaza masarautar Kano, da kuma tsige sarkin da al’ummar Kano ke matukar girmamawa.