Home Labaru Kiwon Lafiya Ta’ddanci: Kimanin Mutane 168 Ne Su Ke Mutuwa A Kowacce Rana A...

Ta’ddanci: Kimanin Mutane 168 Ne Su Ke Mutuwa A Kowacce Rana A Yamen

331
0

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce a duk sa’a guda kimanin mutane 7 ke mutuwa a kasar Yamen.

Kungiyar ta kuma sanar da cewa, kasar Yamen ita ce kasa da ta fi kowacce kasa talauci a yankin Gabas ta Tsakiya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, iyaye mata da yara kanana sun fi kowa shiga tashin hankali duk da cewa kungiyoyi na bada tallafi wajen ganin an magance matsalar.