Home Labaru Boko Haram Ta Kunshi Kabilu Da Dama A Nijeriya – Zulum

Boko Haram Ta Kunshi Kabilu Da Dama A Nijeriya – Zulum

661
0
Babagana Umara-Zulum, Gwamnan Jihar Borno
Babagana Umara-Zulum, Gwamnan Jihar Borno

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara-Zulum, ya ce a halin yanzu mutane daga kabilun kasar nan da dama ne ke cikin kungiyar Boko Haram, sabanin kabila guda da a baya ake danganta su da ita.

Babagana Zulum ya shaida wa manema labarai haka ne, bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari fadar sa da ke Abuja.

Ya ce muddin ana son gaggauta kawo karshen matsalar Boko Haram, dole a dauki matakan warware matsalolin da su ka haifar da tada kayar bayan, da kuma batutuwan da ke karfafa kungiyar Boko Haram.

Gwamna Zulum ya kara da jaddada bukatar kara yawan jami’an tsaro a kauyukan da ke fadin jihar Borno, da kuma bukatar girke dakarun a wuraren da babu su a baya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/libertytvnews

Twitter: https://twitter.com/libertytvnews

Instagram: https://instagram.com/libertytvng

Liberty Radio 103.3 FM Abuja Kai Tsaye A Yanar Gizo ??

zeno.fm/libertyradioabuja

Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna Kai Tsaye A Yanar Gizo ??
zeno.fm/tasharyancikaduna ?

Kira ??? +1-701-719-6971 don suraren (Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna) kai tsaye ta wayar hannu. Musamman Ga Waɗanda Suke Ƙasar Amurka.

Kuna iya turo mana labari ko shawara a: info@libertytvradio.com