Home Labaru Ba Za Mu Yarda Da Karin Farashin Wutar Lantarki Ba – NLC

Ba Za Mu Yarda Da Karin Farashin Wutar Lantarki Ba – NLC

793
0
Kungiyar Kwadago Ta Nijeriya, NLC
Kungiyar Kwadago Ta Nijeriya, NLC

Kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, ta yi Allah-Wadai da yunkurin kara farashin wutar lantarki da kamfanonin da su ka sayi NEPA su ka fara.

Sakataren kungiyar Emmanuel Ugboaja, ya ce ma’aikatan Nijeriya ba za su amince da wannan sabon tsari na karin farashin wutar lantarki ba.

A wani bangare kuma, Ugboaja ya bayyana wa manema labarai cewa, kungiyar ma’aikatan ba ta amince da kokarin sake sayen kamfanin NEPA daga hannun ‘yan kasuwa da gwamnatin tarayya ke shawarar yi ba.

Idan dai ba a manta ba, Hukumar kula da wutar lantarki ta Nijeriya, ta tabbatar da karin farashin wutar latarki da kamfanonin da su ka sayi kamfanin NEPA su ka bukata a fadin Nijeriya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/libertytvnews

Twitter: https://twitter.com/libertytvnews

Instagram: https://instagram.com/libertytvng

Liberty Radio 103.3 FM Abuja Kai Tsaye A Yanar Gizo ??

zeno.fm/libertyradioabuja

Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna Kai Tsaye A Yanar Gizo ??
zeno.fm/tasharyancikaduna ?

Kira ??? +1-701-719-6971 don suraren (Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna) kai tsaye ta wayar hannu. Musamman Ga Waɗanda Suke Ƙasar Amurka.

Kuna iya turo mana labari ko shawara a: info@libertytvradio.com

Leave a Reply