Home Labaru Boko Haram: Sojoji Sun Kwashe Mazauna Garin Da Ake Zargin Boko Haram...

Boko Haram: Sojoji Sun Kwashe Mazauna Garin Da Ake Zargin Boko Haram Na Mafaka

370
0

Hukumar Tsaro ta Sojin Nijeriya, ta umarci mazauna kauyen Jakana su gaggauta ficewa daga garin gaba daya, biyo bayan yawaitar samun rahotannin cewa Boko Haram na shiga cikin garin su na boyewa.

Kauyen Jakana dai ya na da tazarar kilomita 40 tsakanin sa da birnin Maiduguri na Jihar Borno.

Bayan wani hari da aka kai garin a cikin watan Disamba, Boko Haram sun sake yin galabar shiga garin a cikin Janairun da ya gabata, inda su ka banka wa sansanin sojiji da ofishin ‘yan sanda wuta.

A ranar Talatar da ta gabata, an rika ganin motoci kirar bas cike da mutanen Jakana a na sauke su a Sansanin Masu Gudun Hijira na Bakasi.

Kakakin ‘Operation Lafiya Dole’ Ado Musa, ya ce an kwashe mazauna garin zuwan sansanin gudun hijira ne domin yin sintirin kakkabe Boko Haram a yankin.

Ya ce da zarar an kammala aikin za a gaggauta maida kowa gidan sa.

Leave a Reply