Home Labaru Dambarwar Majalisa: Sanatocin APC 36 Ke Goyon Bayan Sanata Ali Ndume

Dambarwar Majalisa: Sanatocin APC 36 Ke Goyon Bayan Sanata Ali Ndume

271
0

Akalla sanatoci 36 na jam’iyyar APC ke goyon bayan Sanata Ali Ndume, a matsayin dan takarar kujerar shugaban majalisar dattawa kamar yadda wani zababben sanata da ya nemi a sakaya sunan shi ya bayyana.

Zababben sanatan ya bayyana haka ne, yayin da ya ke zantawa da manema labarai a wajen taron ilmantar da sabbin ‘yan majalisa a Otal din Transcorp Hilton da ke Abuja.

Idan dai za a iya tunawa, duk da cewa jam’iyyar APC ta mara wa Sanata Ahmed Lawan baya, amma Sanata Ndume ya lashi takobin ci-gaba da takarar sa.

Zababben sanatan, ya ce akwai kimanin zababbun sanatoci 36 da ke goyon bayan Ndume, kuma hakan ya faru ne saboda yadda su ke gudanar da shirin zaben kujerar shugaban majalisa.

Leave a Reply