Home Labaru Boko Haram: Shekau Ya Sake Fitar Da Wani Sabon Sakon Murya

Boko Haram: Shekau Ya Sake Fitar Da Wani Sabon Sakon Murya

924
0
Abubakar Shekau, Shugaban Kungiyar Boko Haram
Abubakar Shekau, Shugaban Kungiyar Boko Haram

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya sake fitar da wani sabon sakon murya, inda ya yi barazanar kai ma wani lauyan Nijeriya mazaunin kasar Ingila Audu Bulama Bukarti hari.

Bukarti dai kwararren mai nazari ne a Cibiyar Tony Blair da ke jagorantar wata tawagar masu bincike a kan ayyukan kungiyoyin masu tsatsauran ra’ayi a Afirka, musamman Boko Haram na tsawon shekaru 10.

Lauyan ya maida hankali ne wajen amfani da hujojji daga cikin littattafan addinin Musulunci wajen yaki da tsauraran ra’ayoyi, ya kuma wallafa wata takarda mai taken ‘Cikakken bayani a kan Boko Haram’, inda ya yi fashin baki game da kungiyar, tare da samar da hujojjin da za a iya amfani da su don kawar da tsaurarran ra’ayoyin da kungiyar ke koyarwa.

A cikin sakon muryar mai tsawon mintuna biyar da ya yi wa lakabi da ‘Martanin Shekau zuwa ga azzalumi Bulama Bukarti’, Shekau ya ce Bukarti ya shiga uku, kuma daga yanzu sun sa kafar wando guda.