Home Labaru ‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 6 Da Ake Zargi Da Kisan Shugaban...

‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 6 Da Ake Zargi Da Kisan Shugaban PDP Na Rivers

353
0
Nnamdi Omoni, Mai Magana Da Yawun Rundunar ‘Yan Sanda Ta Jihar Rivers
Nnamdi Omoni, Mai Magana Da Yawun Rundunar ‘Yan Sanda Ta Jihar Rivers

Sashen musamman na binciken laifuffukan kisan-kai na hukumar ‘yan sanda ta jihar Rivers, sun tabbatar da kammala bincike a kan mutane shida da ake zargi da kisan wani shugaban jam’iyyar PDP a karamar hukumar Obio-Akpor ta jihar Rivers.

Kamar yadda hukumar ta sanar, za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu, bisa kama su da hannu a kisan shugaba Anele Nworzuruka, wanda aka harbe a gaban matar sa da ‘ya’yan sa uku a ranar 21 ga watan Satumba na shekara ta 2019.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Rivers Nnamdi Omoni, ya ce an kama mutane shidan da ke da hannu a kisan.

Ya ce wadanda ake zargin an kama ne a lokuta daban-daban, kuma sun bayyana cewa su ‘yan kungiyar asiri ce ta Iceland da su ka addabi jama’ar karamar hukumar Obio/Akpor ta jihar.

Daya daga cikin wadanda ake zargin Bright Wali, ya ce shi ya jagoranci kungiyar zuwa gidan wanda su ka kashe ta hanyar harbi da bindiga.

Leave a Reply