Asusun kula da kananan yara na ajalisar dinkin duniya UNICEF, ta bayyana da cewa ta’addancin Boko Haram ya kassara yara 432 a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya cikin shekarar 2018 da ta gabata.
Babbar jami’ar sadarwa ta asusun Unicef, Eva Hinds, ta bayyana haka a cikin wata sanarwa, a yayin tunawa da sace ‘yan mata fiye da 100 na makarantar sakandire ta garin Chibok dake jihar Borno shekaru biyar da suka gabata.
Ta ce ta’addancin kungiyar Boko Haram ya salwantar da rayukan kananan Yara 432, garkuwa da 180, gami da kananan yara Mata 43 da aka ke ta masu haddi da cin zarafi cikin shekarar bara a yankin Arewa maso Gabas. Hinds, ta bayyana cewa, kungiyar Boko Haram ta yaudari kananan yara fiye da 3,500 wajen cin kasuwar ta’addanci na kai hare-hare a shekara ta 2013 zuwa yanzu.
You must log in to post a comment.