Home Labaru Kare Aukuwar Haddura: Hukumar FRSC Ta Yi Gargadi Ga Masu Zuwa...

Kare Aukuwar Haddura: Hukumar FRSC Ta Yi Gargadi Ga Masu Zuwa Jihar Zamfara

314
0

Hukumar kare aukuwar haddura kasa reshen jihar Zamfara ta gargadi masu zuwa shan maganin bindiga a Zamfara su guji lodin da ya wuce kima domin gudan aukuwar hadari..

Mataimakin kwamandan hukumar na jihar Zamfara, Iro Danladi ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a hedikwatar su da ke Gusau.

Kwamandan Iro Danladi, ya bayyana takaicinsa ga masu lodin da ya wuce, musamman masu zuwa shan magani, sanadiyyar haka ya sa wasu su kai hadari mutum ashirin su ka mutu, wanda hakan ya nuna cewar garin nemna kiba,  an nemo rama.

Kwamandan ya ce hukumar ba za ta lamunci ganganci da rayuwar mutane ba, duk wanda aka kama da saba dokokin tuki zai gamu da hukuncin biyan tara. Daga karshe  ya yi kira ga masu abubuwan hawa  su kasance masu bin doka da oda da kula da lafiyar abubuwan hawa domin kaucewa shiga hadurra.