Home Labaru Sudan: Sabon Shugaban Mulki Soji Zai Kafa Gwamnatin Farar Hula

Sudan: Sabon Shugaban Mulki Soji Zai Kafa Gwamnatin Farar Hula

612
0

Sabuwar gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin Soji a Sudan ta yi alkawarin samar da gwamnatin farar hula cikin kasa da shekaru biyu, bayan tattaunawa da bangaren gwamnati mai barin gado da kuma jagororin adawar kasar, dai dai lokacin da masu zanga-zanga ke ci gaba da boren matakin.

Cikin wani jawabin kai tsaye ta gidan Talabijin din kasar karon farko da ya gabatar Laftanal Janar Abdel Fattah al-Burhan Abdelrahman da ke matsayin shugaba a yanzu, ya ce ya janye dokar haramta zirga-zirgar cikin dare, haka zalika ya yi umarnin sakin ilahirin fursunonin siyasa da gwamnatin tsohon shugaban kasar Omar al Bashir ta daure.Bayan nasarar soji ta Hambarar da gwamnatin al Bashir a ministan tsaron kasar Awad Ibn Auf da tun farko ya dare kujerar shugabancin kasar ya yi murabus da kuma shugaban sashen fikira na kasar Salah Abdallah Mohemmed Saleh, wanda ake zargi da umarnin kashe-kashen da ya faru yayin zanga-zangar watanni 4 da ta gudana a kasar.

Leave a Reply