Home Labaru Boko Haram Na Barazana Ga Makarantun Boko A Jihar Neja

Boko Haram Na Barazana Ga Makarantun Boko A Jihar Neja

101
0

Gwamnatin jihar Neja, ta ce wasu da ta ke sa ran ‘yan ƙungiyar Boko Haram ne, su na barazana ga iyayen ɗalibai su janye ‘ya’yan su daga zuwa makarantun Boko.

Rahotanni sun ambato sakataren gwamnatin jihar Ahmed Ibrahim Matane ya na cewa, mayaƙan su na barazana ne a yankukan Kwaki da Kusaso da Kawure da Chikuba da Kurebe da Madaka da Farin-Dutse da Falali da kuma Ibbru.

Tun da farko dai gwamnatin jihar Neja ta ce, ‘yan Boko Haram sun mamaye wasu yankuna na ƙananan hukumomin Kaure da Shiroro.