Home Labaru Dattawan Arewa Sun Gargadi Buhari Kan Yi Wa Nnamdi Kanu Afuwa

Dattawan Arewa Sun Gargadi Buhari Kan Yi Wa Nnamdi Kanu Afuwa

73
0

Kungiyar tuntuba ta al’ummomin Arewa, ta ce bai dace a yi wa shugaban kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu afuwa ba.

Sakataren yada labarai na kungiyar Emmanuel Yawe, ya ce ba za a iya yarda da Nnamdi Kanu ba, don haka ya ja kunne a kan duk wani yunkurin gwamnati na yafe ma shi.

Emmanuel Yawe ya bayyana haka ne a lokacin da ya yi hira da Jaridar Punch, inda ya ce abin da ya kamata shi ne a bar shari’a ta yi aiki, tunda gwamnatin Nijeriya ta na aiki ne da tsarin mulki.

Yawe ya maida martani ne ga wasu daga cikin dattawan kabilar Igbo, wadanda su ka je wajen shugaban kasa su na neman a yi wa Nnamdi Kanu afuwa.