Home Labarai ‘Yan Bindiga Sun Sako Hakimi Sun Rike Farfesan Da Ya Kai Kudin...

‘Yan Bindiga Sun Sako Hakimi Sun Rike Farfesan Da Ya Kai Kudin Fansa

17
0

Rahotanni daga Jihar Kano na cewa, Hakimin Karfi da ke karamar hukumar Takai Abdulyahyah Ilo da aka sace ya samu ‘yanci daga hannun wadanda su ka yi garkuwa da shi.

‘Yan bindigar, sun rike karamin farfesa a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano Huzaifa Karfi, wanda rahotanni su ka ce ya je ne domin ya kai kudin fansa.

Wata majiya ta ce, ‘yan bindigar sun kashe mutane shida da su ka yi kokarin ceto basaraken a lokacin da su ka yi awon gaba da shi.

Wani mazaunin yankin mai suna Musa Sa’ad ya tabbatar da sakin basaraken, inda ya ce mafarauta da ’yan banga sun kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne da ke da nasaba da sace-sace a kauyen Karfi.

Majiyar ta ce, ‘yan bindigar sun karbi kudin fansa tare da tsare Huzaifa saboda da mutumin da ‘yan banga suka kama, inda su ka bukaci a sako mutumin su a matsayin shara]in sakin sa.

Sai dai Kakakin rundunar ’yan sanda ta Jihar Kano SP Abdullahi Kiyawa bai iya tabbatar da faruwar lamarin ba, amma ya yi alkawarin bada bayani idan ya samu.