Home Home Birtaniya Ta Janye Gargadin Yiwuwar Harin Ta’addanci A Birnin Abuja

Birtaniya Ta Janye Gargadin Yiwuwar Harin Ta’addanci A Birnin Abuja

480
0
Kasar Birtaniya ta janye gargadin da ta yi wa al’ummar ta game da yiwuwar hare-haren ta’addanci a birnin tarayya Abuja, inda ta ce a yanzu al’amurra sun fara daidaita a birnin saboda daukar matakan kawar da barazanar da mahukuntan kasar su ka y

Kasar Birtaniya ta janye gargadin da ta yi wa al’ummar ta game da yiwuwar hare-haren ta’addanci a birnin tarayya Abuja, inda ta ce a yanzu al’amurra sun fara daidaita a birnin saboda daukar matakan kawar da barazanar da mahukuntan kasar su ka yi.

Makonni biyu bayan Ofishin jakadancin Birtaniya ya bi sahun takwarorin sa na Amurka da Italiya wajen gargadin al’ummomin su da ke rayuwa a Nijeriya, cewa su kaurace wa ziyartar wasu sassan Nijeriya musamman birnin Tarayya Abuja game da yiwuwar hare-haren ta’addanci, Ofishin ya ce a yanzu barazanar ta shude a birnin Abuja, sai dai har yanzu babu cikakken tsaro.

Wata sanarwa da ofishin kula harkokin ci-gaban kasashe renon Ingila ya wallafa a shafin san a yanar gizo, Birtaniya ta ce ta janye batun hana al’ummomin ta bulaguro zuwa Abuja, duk da cewa har yanzu akwai barazanar tsaro, sai dai ta ce har yanzu hanin ya na nan a kan sauran sassan Nijeriya musamman jihohin arewa.

Ofishin kula da kasashe rainon Ingila, ya sabunta gargadi a kan ziyartar jihohin Borno da Yobe da Adamawa da Gombe da Kaduna da kuma Katsina, baya ga Zamfara da Delta, da Bayelsa da Rivers da Akwa Ibom da kuma Cross River, wadanda ya ce su na fama da barazanar hare-haren ta’addanci .

LEAVE A REPLY