Home Labarai Sojoji Sun Kashe Kwamandan Boko Haram Sun Cafke 27

Sojoji Sun Kashe Kwamandan Boko Haram Sun Cafke 27

47
0

Sojoji sun kashe shahararren dan ta’addan Boko Haram Lawan Yashin, tare da kama wani dauke da katunan zabe 67 a wani sananin gudun hijira da ke Jihar Borno.

Hedikwatar Rundunar Operation Hadin Kai tare da hadin gwiwar dakarun CJTF, ta ce sun kashe Lawan Yashin tare da kama wani Burama Modu dauke da katunan zabe 67 na dindindin a Maiduguri.

Daraktan yada labarai na tsaro Manjo-Janar Danmadami Musa, ya ce an kashe Lawan Yashin ne lokacin da ya ke kokarin tserewa, bayan ya ga sojoji tare da wasu 19 daga cikin abokan ta’addancin sa a sansanin ’yan gudun hijira da ke Shuwari a Karamar Hukumar Maiduguri.

Manjo-Janar Danmadami Musa, ya ce an kuma kama mutane 27 da ake zargin ’yan Boko Haram da ISWAP ne, tare da kwato makamai da alburusai da dama a hannun su.