Home Labaru Binciken Pandora Papers: Borin-Kunyar Peter Obi Bayan Premium Times Ta Fallasa Harƙallar...

Binciken Pandora Papers: Borin-Kunyar Peter Obi Bayan Premium Times Ta Fallasa Harƙallar Sa

5
0
Tsohon Gwamnan jihar Anambra Peter Obi ya maida martani ga PREMIUM TIMES, bayan an buga labarin yadda ya riƙa karya dokoki yana waske wa biyan haraji ta hanyar haramtacciyar hada-hadar da ya riƙa yi a waje.

Tsohon Gwamnan jihar Anambra Peter Obi ya maida martani ga PREMIUM TIMES, bayan an buga labarin yadda ya riƙa karya dokoki yana waske wa biyan haraji ta hanyar haramtacciyar hada-hadar da ya riƙa yi a waje.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Peter Obi ya shekara uku ya na gudanar da harƙalla ta ɓarauniyar hanya da kauce wa dokar hada-hada.

Jaridar ta ce Obi ya ci gaba da riƙe muƙamin sa na Darakta, a kamfanin sa da ke Birtaniya, mai suna NEXT International UK Limited, har tsawon watanni 14 bayan rantsar da shi Gwamnan Jihar Anambra kuma hakan ya karya dokar sashe na shida na dokar tsarin aiki ta Najeriya.

Ta kara da cewa Obi ya yi amfani da wasu dabaru inda ya ɓoye kamfanonin sa da ke ƙasashen waje, waɗanda shi da kan sa ya yarda cewa bai bayyana su ba a cikin kadarorin sa a lokacin da ya cika fam ɗin takarar gwamna, kamar yadda dokar Najeriya ta tanadar, kuma yin hakan ya karya sashe na 11 kundi na biyar na Dokar 1999.

Jaridar t ace Peter Obi, ya yi amfani da asusun Ƙasashen Waje a matsayin sa na gwamna, wanda haramun ne a dokar Najeriya kuma duk ya kasa kare wannan fallasa da aka yi masa. A martanin da Kakakin Yaɗa Labaran Peter Obi Valentine Obienyem ya aiko wa PREMIUM TIMES, ya haƙiƙice cewa bai karya dokar Najeriya