Home Labaru Yajin Aiki: Kungiyar Direbobin Tanka Ta Bayyana Shirin Ta

Yajin Aiki: Kungiyar Direbobin Tanka Ta Bayyana Shirin Ta

5
0
Kungiyar direbobin motocin dakon mai a Najeriya NUPENG ta shirya fara yajin aikin gama gari daga yau litinin domin bayyana damuwar ta dangane da lalacewar hanyoyin mota a fadin Najeriya.

Kungiyar direbobin motocin dakon mai a Najeriya NUPENG ta shirya fara yajin aikin gama gari daga yau litinin domin bayyana damuwar ta dangane da lalacewar hanyoyin mota a fadin Najeriya.

Shugaban kungiyar na yankin kudu maso yammacin Najeriya Tayo Aboyeji ya bayyana shirin, inda yake cewa kungiyar tayi asarar direbobi da dama tare da kadarori sakamakon lalacewar hanyoyin.

Aboyeji yace yajin aikin zai shafi kasa ne baki daya.

Yace sun dade suna bayyana shirin yajin aikin, amma suke dakatarwa saboda tunanin irin illar da zai haifarwa  ‘yan kasa.

Shugaban kungiyar yace a halin da ake ciki yanzu, tankar mai kan kwashe kwana 5 zuwa 6 idan tayi dakon mai daga Lagos zuwa Abuja saboda tabarbarewar hanyoyin, wanda ya bayyana shi a matsayin abin kunya ga Najeriya.

Aboyeji yace kokarin su na janyo hankalin gwamnati a kan lalacewar hanyoyin yaci tura, bayan Lalacewar hanyoyin na daya daga cikin abinda barayi da ‘yan bindiga ke amfani da shi suna yiwa mutane fashi da kuma garkuwa da jama’a.