
Gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers ya ayyana muradin sa na neman shugabancin Najeriya, yana mai cewa yana da ƙwarewar da zai lashe zaɓen 2023 a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar adawa ta PDP.
Gwamna Wike, ya bayyana haka ne yayin ganawar da ya yi da shugabannin jam’iyyar PDP na Jihar Benue a gidan gwamnatin jihar da ke Mukudi a ranar Lahadi.
Wike, ya nemi wakilan jam’iyyar su jefa masa ƙuri’a a zaɓen fitar da gwani yana mai jaddada batun karɓa-karɓa.
Ya ce matukar ana bukatar korar jam’iyyar APC daga kan karagar mulki, to shi kadai ne zai iya.
Ya ƙara da cewa dole ne su ƙwace mulki, kuma ya shirya yin hakan a jam’iyyar PDP domin Allah yana tare da su, shi ya sa APC ke taɓarɓarewa a koyaushe.