Home Labaru Bincike: Magu Ya Yi Ikirarin Bai Wa Ma’aikatu Da Majalisa Wasu Kadarori.

Bincike: Magu Ya Yi Ikirarin Bai Wa Ma’aikatu Da Majalisa Wasu Kadarori.

403
0

Dakataccen mukaddashin shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu ya yi ikirarin bai wa wasu daga cikin ma’aikatu da sassan gwamnati dama Majalisar kasa wani bangare na motoci da kadarorin da ya kwato daga hannun wadanda suka sace dukiyar kasa.

Da yake bayani a gaban kwamitin binciken Ibrahim Magu ya ce maimakon shigar da bayanan kadarorin da ya kwato ko kuma sanya kudin cikin asusun bai daya na gwamnatin tarayya, ya raba wani bangare na kudaden ne ga daidaikun mukarraban gwamnati da kuma ma’aikatu.

A makon jiya ne Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da Magu inda aka fara tuhumarsa, karkashin tawagar bincike ta musamman bisa jagorancin tsohon shugaban kotun daukaka kara ta kasa Ayo Salami.

Rahotanni sunce bayan tarin tambayoyin da Magu ya amsa kan karkatar da kudade daga karshe, dakataccen shugaban hukumar EFCC ya musanta zargin da ministan shari’a Abubakar Malami yayi a kansa.