Home Labaru Yaki Da Rashawa: Kungiyar ‘Yan Sintiri Ta Kafa Wani Kwamati

Yaki Da Rashawa: Kungiyar ‘Yan Sintiri Ta Kafa Wani Kwamati

278
0

Kungiyar ‘yan sitiri ta Kasa karkashin jagorancin Navy Captain Umar Abubakar Bakori, ta bukaci manbobinta su taimaka mata da  mahimman bayanai da za su taimaka wajen gano yadda wanda ya ke sojan gona wajen bayyanna kanshi a matsayin shugaban kungiyar  Alhaji Usman Muhammade Jahun ya tafiyar da asusun kungiyar.

Kwmadan kungiyar ya bayyana hakan ne a lokacin   da yake magana da manema labarai a Kaduna, bayan kafa wani kwamitin bincike na mambobin kungiyar  wadanda za su fara binciken.

Ya ce kwamitin ne zai yi bincike kudin da kungiyar ‘yan sintitri ta Najeriya ta samu a lokacin da Usman Jahun ke bayyana akan shi a matsayin kwamandan ta, zamanin marigayi Alhaji Ali Sokoto.

Navy Capatain Umar Abubakar Bakori, ya ce shi a matsayin shi na kwamandan kungiyar mai ci, bai da wata matsala da Usman Jahun.

Haka zalika kwamitin zai yi amfani da kundin tsarin kungiyar ‘yan sintiri ta Najeriya domin sauke nauyin da ya rataya a wuyan sa.

Daga karshe kwamandan Navy Captain Abubukar Usman Bakori, ya bukaci Alhaji Usman Muhd Jahun  ya daina bayyana kan shi da duk wani mukamin na kungiyar.