Home Labaru Kiwon Lafiya Iftila’i: Tankar Mai Hallaka Mutum 20 A Yankin Niger Delta

Iftila’i: Tankar Mai Hallaka Mutum 20 A Yankin Niger Delta

229
0

Akalla mutane 20 ne suka mutu bayana da wata Tankar Mai ta kama da wuta a yankin Niger Delta.

Lamarin ya faru a jiya Laraba a kan babbar hanyar da ke haɗa jihar Edo da kuma jihar Delta.

Wasu daga cikin mutanen sun ƙone ƙurmus yadda ba za a iya gane su ba.

Shedun gani da Ido sun bayyana cewa galibin waɗanda suka mutu sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke ƙokarin ɗiban mai daga motar bayan da ta fadi.

Daga bisani wutar ta yadu zuwa kan hanya kuma ta kama wasu daga cikin motocin da ke wucewa a kan hanyar.

Wani jami’in gwamnatin jihar Delta ya ce tirelar ta kife ne a lokacin da take kokarin kwana sannan daga bisani ta kama da wuta.