Gwamnatin tarayya, ta ba shugabannin kasashen duniya tabbacin ba su tsaro a lokacin a ranakun 29 ga watan Mayu da 12 ga watan Yuni na shekara ta 2019.
Ministan Labarai da Al’adu Lai Mohammed ya bayyana wa manema labarai haka a Abuja.
Ya ce Nijeriya za ta ba kowane shugaban kasa da zai zo bikin rantsar da shugaba Muhammadu Buhari da mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo tsaro a ranar 29 ga watan Mayu.
Lai Mohammed ya kara da cewa, gwamnatin tarayya ta bayyana 29 ga watan Mayu da 12 ga watan Yuni a matsayin ranakun hutu. Wannan sanarwa dai ta biyo bayan bikin rantsar da shugaba kasa Muhammadu Buhari da za a yi karo na biyu, yayin da Nijeriya ke fama da gagarumar matsalar tsaro a kowane lungu da sako.
You must log in to post a comment.