Home Labaru Harin Ta’addanci: Masu Ikirarin Jihadi A Mali Sun Kashe Sojan Nijeriya Guda

Harin Ta’addanci: Masu Ikirarin Jihadi A Mali Sun Kashe Sojan Nijeriya Guda

784
0

Rahotanni sun tabbatar da mutuwar wani sojan Nijeriya guda tare da jikkata wasu biyu a wani da aka kaiwa sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali.

Wasu ‘yan bindiga ne suka kai harin kan dakarun a garin Timbuktu da ke arewacin kasar, yankin da ke cike da kungiyoyin sa kai masu yawa.

Mai Magana da yawun sakataren Majalisar ta Dinkin Duniya, Antonio Guterres, Stephane Dujarric ya ce kawo yanzu ba a ga tabtabatar da wadanda suka kai harin ba.

A harin dai, an jikkata wasu sojojin samar da zaman lafiyan uku ‘yan kasar Chadi a garin Tessalit da ke arewacin yankin Kidal, kusa da iyakar kasar Algeriya a lokacin da motar su ta taka wata nakiya.

Antonio Guterres ya nuna jimamin sa da kuma mika ta’aziyyar sa ga iyalai da gwamnatin Nijeriya, tare da yin fatan samun sauki ga sojojin Nijeriya da aka jikkata a harin, sannan suma sojojin kasar Chadin da aka jikkata a lokacin da motar ta taka nakiya ya yi masu fatan samun daukin cikin hanzari.

A karshe gwamnatin tarayya ta yi Allah-wadai a kan harin da a ka kai a kan tawagar sojojin Majalisar Dinkin Duniya wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Sojan Nijeriya guda.

Leave a Reply