Home Labarai Bikin Gargajiya: Auren Ɗan Shekara 63 Da ‘Yar 12 Ya Harzuƙa Mutane...

Bikin Gargajiya: Auren Ɗan Shekara 63 Da ‘Yar 12 Ya Harzuƙa Mutane A ghana

42
0


Wani hamshaƙin ɗan gargajiya mai shekara 63 ya fusata jama’a
a Ghana bayan ya auri wata yarinya ‘yar shekara 12.
Bokan Nuumo Borketey Laweh Tsuru XXXIII, ya yi auren ne a
wani bikin al’ada da aka yi ranar Asabar.


Sakamakon caccaka ne kuma, shugabannin al’umma suka fito suna cewa mutane ba su fahimci al’adun gargajiyarsu ba Mafi ƙarancin shekarun aure bisa doron doka a Ghana shi ne 18 kuma an samu raguwar yawan auren wuri a ƙasar, amma lamarin na ci gaba da faruwa nan da can.


A cewar wata ƙungiya Girls Not Brides, mai rajin kawar da auren wuri, kashi 19% na ‘yan matan ƙasar ne aka yi musu aure kafin su kai shekara 18.


Bidiyo da hotunan gagarumin shagalin bikin na ranar Asabar wanda gomman jama’ar yankin suka halarta, sun karaɗe shafukan sada zumunta, lamarin da ya harzuƙa da yawan al’ummar Ghana.


Masu sukar lamarin sun yi ta kira ga hukumomi su rusa auren sannan su gudanar da bincike a kan Mista Tsuru.

Leave a Reply