Gwamnatin Najeriya ta sanar karin kudin wutan lantarki da fiye da kashi 300 cikin 100 ga masu amfani da wutar ta lantarki.
Sabon farashin da hukumar kula da da harkokin kamfanonin da ke rarraba wutan lantarki ta sanar a Abuja ya nuna cewa gwamnatin ta amincewa kamfanonin su kara kudin wutan ne daga Naira 68 kowane kilowatt na lantarki zuwa Naira 225.
Mataimakin shugaban hukumar kula da sa ido a harkar wutan lantarki Musliu Oseni ya sanar da cewa wannan kari ne da ya shafi masu amfani da wutar lantarkin da ke biranen da ke samun wutan lantarki na tsawon sao’i 20 a kowace rana.
Gwamnatin Najeriya dai ta sanar da karin farashi wutan lantarkin ne da kusan kashi 300 a daidai lokacin da al’ummar kasa ke ci gaba da bayyana damuwa sakamakon matsalar tsadar rayuwa, da kuma karin farashin man fetur da suke fama da shi.
Sai dai tuni kungiyar kwadago ta Najeiya NLC ta bayyana rashin amincewar ta da wannan kari, inda ta ce za ta yi fito na fito da shi.