Rundunar sojin Nijeriya, ta ce dakarun ta sun kashe wani dan
kungiyar IPOB a yankin Ihioma da ke karamar hukumar Orlu a
jihar Imo.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Birgediya
Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ta ce lamarin ya faru ne a
ranar Lahadin da ta gabata.
Sanarwar ta kara da cewa, dakarun ta sun kai farmaki a kan ‘yan
kungiyar, sun kuma yi musayar wuta a wata hanya da ake kira
Banana Junction, daya daga cikin yankunan da IOPB ta tilasta
wa mutane su rika zaman gida.
A musayar wutar ne dakarun su ka yi nasarar kashe kwamandan
kungiyar IPOB, lamarin da ya sa sauran su ka tsere.
Sojojin dai sun cigaba da neman wadanda su ka tsere, wadanda
ke tada zaune-tsaye da hana mazauna yankin sakat.
Sai dai rundunar sojin ta ce, ‘yan kungiyar IPOB sun fara yada
wani bidiyon farfaganda don jama’a su tausaya masu, inda su ka
bukaci a yi watsi da shi.














































