Home Labaru Biafra: Rikici Ya Barke Bayan Sojoji Sun Bindige ‘Yan Kungiyar Awaren IPOB

Biafra: Rikici Ya Barke Bayan Sojoji Sun Bindige ‘Yan Kungiyar Awaren IPOB

5
0
An samu tashin hankali a garin Arochukwu na jihar Abia, yayin da jami’an tsaro ke fafatawa da ‘yan kungiyar awaren Biafra ta IPOB a yankin.

An samu tashin hankali a garin Arochukwu na jihar Abia, yayin da jami’an tsaro ke fafatawa da ‘yan kungiyar awaren Biafra ta IPOB a yankin.

Wani rahoto da ba a tabbatar da shi ba ya nuna cewa, mutane hudu da ake zargin ‘yan kungiyar IPOB ne ana fargabar an kashe su yayin fafatawar.

Duk da cewa har yanzu ba a tabbatar da abin da ya janyo harbe-harben ba, wata majiya daga yankin ta ce daga jin labarin an kai shugaban IPOB Nnamdi Kanu kotu a Abuja domin fuskantar shari’a ne wasu ‘yan kungiyar su ka hau kan tituna sun a ihu.

Majiyar ta ce, ‘yan kungiyar IPOB sun nuna farin cikin cewa Nnamdi Kanu ya na raye, sabanin rahotannin da su ke samu game da lafiyar sa.

Wasu rahotanni da ba a tabbatar da ingancin su ba, sun ce yayin da sojoji su ka fuskanci ‘yan kungiyar IPOB da ke cikin jerin gwanon, nan take rikici ya barke har aka bindige ‘yan kungiyar biyar, lamarin da ya sa mazauna garin su ka yi ta tserewa domin tsira da rayukan su.