Home Labaru Amincewa Da Al’adun Faransawa: Musulmai A Faransa Sun Koka Kan Matsa Musu...

Amincewa Da Al’adun Faransawa: Musulmai A Faransa Sun Koka Kan Matsa Musu Da Ake Yi

106
0

A cikin makon nan ne Majalisar Musulman ƙasar Faransa (CFCM) ke shirin ganawa da Shugaba Emmanuel Macron, don tabbatar da sabuwar ƙasidar ‘dokar al’adun Faransa” ga limamai a ƙasar don su rattaba hannu.

An bayar da rahoton cewa an buƙaci Majalisar ta (CFCM), wacce ta ƙunshi ƙungiyoyi daban-daban na Musulmai a ƙasar da su haɗa a cikin ƙasidar mai ƙunshe da dokar al’adun Jamhuriyyar Faransa, yin watsi da Musulunci a matsayin ƙungiyar siyasa da kuma hana tasirin ƙasashen waje.

Chems-Eddine Hafiz, mataimakin shugaban ƙungiyar ta CFCM kuma shugaban babban masallacin birnin Paris y ace dukkannin su ba su amince da ko mece ce dokar a’ladun Faransa da abin da ta ƙunsa ba.

Amma kuma, ya ce, suna cikin yanayi na tarihin sauyi ga addinin Islama a Faransa kuma mu Musulmai na fuskantar nauyin da ya rataya a wuyan su Shekaru takwas da suka gabata, inda yace tunanin sa daban ne.