Tsohuwar ministar man fetur Diezani Alison Madueke ta karyata zargin da ake yi mata na cewa ta saci kudin Najeriya.
Karanta Wannan: Hajjin Bana: Za A Fara Jigilar Dawo Da Alhazan Nijriya Ranar 17 Ga Watan Agusta
Diezani Alison ta ce ko sisin kobo ba ta sata a Najeriya ba, kuma idan akwai mutumin da yake da hujja ya fito ya bayyana.
Tsohuwar ministar ta nuna rashin jin dadinta da irin zagin da ‘yan Najeriya suke yi mata, inda ta karyata zargin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da hukumar EFCC suka yi mata na cewar ta yi sama da fadi da dukiyar talakawar Najeriya a lokacin da take aiki.
Diezani ta karyata zargin cewa ta yi almubazzaranci da dukiyar man fetur kamar sauran takwarorinta da kuma wasu manyan masu kudi wanda ta yi alaka da su, inda ta ce ita matar Aure ce, kuma bata da dabi’ar Bera.
Daga
karshe tsohuwar ministar ta nemi duk wani wanda yake da hujja akan ta saci kudi
su fito su bayyanawa duniya.
You must log in to post a comment.