Al’umomin wasu yankuna a jihar Sokoto su na zaman ɗar-ɗar, sakamakon wata wasika da ake zargin ta fito daga ‘yan bindiga, inda su ke barazanar ƙaddamar da hare-hare.
Wasiƙar da aka yi da rubutun Hausa kamar yadda wasu jaridu su ka wallafa, ta na ƙunshe da barazanar ƙaddamar da hari a kan yankunan Dange da Shuni da Kwanar Kimba da Rikina.
A cikin wasiƙar da jaridar Punch ta wallafa a shafin ta, marubucin ya yi barazanar cewa sai sun shiga garin, idan kuma sun a ganin ƙarya ce su ajiye ma’aikata su gani.
Zuwa yanzu dai hukumomin jihar Sokoto ba su fitar da wata sanarwa game da barazanar ba.