Home Home Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Zargi Wasu Kasashe Da Rashin Adalci Na...

Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Zargi Wasu Kasashe Da Rashin Adalci Na Kin Sayar Wa Najeriya Makamai

94
0

Babban hafsan tsaron kasa ya nuna damuwar sa kan abin da ya kira rashin adalcin wasu kasashen da ke kin sayar da makaman soji ga Najeriya ta wajen rabewa da bukatar kare hakkin bil’adama.

Kalaman na Janar Christopher Musa na kara jaddada daya daga cikin manyan kalubalen da kasar da ta fi yawan al’umma a nahiyar Afirka ke fuskanta wajen yaki da matsalar tsaro mai cike da sarkakiya.

Jami’an tsaron sun kwashe shekaru da dama suna fuskantar zarge-zargen kashe-kashen ba bisa ka’ida ba da kuma kame ba bisa ka’ida ba. Akwai lokacin da Amurka da sauran manyan masu samar da makamai suka hana sayar da makamai saboda zarge-zargen.

A cikin watan Disamba, akalla fararen hula 85 ne suka mutu a lokacin da wani jirgin sojin Najeriya mara matuki ya kai hari kan jama’a lokacin wani taron addini a Kaduna na yankin arewa maso yammacin Najeriya, wanda shi ne na baya bayan nan cikin jerin irin wadannan lamuran.

Leave a Reply